Kamar dai sauran kasashen Afirka, Jamhuriyar Niger ta rataya rigar mulkin demokradiyya a wuyanta a cikin shekarar 1991, tare da gabatar da babbar mahawarar kasa. Wannan ci gaba, ya assasa kafuwar jam’iyu siyasa masu dama a cikin kasar, da tsara zabubuka cikin walwala da kuma haske a shekarar 1993 da na shekarar 1999 da kuma na shekarar 2004. An samu tabbaccin yanci da hakkin demokradiyya a cikin kundin tsarin mulkin kasa, wanzuwar kungiyoyin fararen hullar kasa da kuma yantata kafofin watsa (…)
Badakalar sabuwar siyasar duniyar bai daya da manyan hukumomin kasa da kasa irinsu su Bankin duniya da Asusun bayar da lamuni FMI da Hukumar cinikayar duniya OMC da dai sauransu, suka shinfida a cikin kasashen duniya, ta fusakanci kalubalen kungiyoyin fararen hulla da dama a Jamhuriyar Niger.
Wannan gwagwarmayar shinfida demokradiyya, ta samo asali daga kishigilar da aka yiwa dalibai, lokacin da suka fita zanga-zangar kwanciyar hankali da limana ta ranar 9 ga watan Februwari na shekarar (…)